1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin farfado da tattalin arzikin Turai

Abdoulaye Mamane Amadou RGB
May 27, 2020

A wannan Laraba Tarayyar Turai ta gabatar da kudirinta na amfani da kimanin Yuro Biliyan 750 don sake farfado da tattalin arzikin nahiyar da ya fuskanci mummunan gibi a sakamakon annobar Coronavirus.

https://p.dw.com/p/3cpBe
Euroschein Banknoten
Hoto: picture-alliance/dpa/E. Cakir

A yayin gabatar da kudirin a dazun nan, Shugabar Hukumar zartasawa ta Kungiyar Ursula von der Leyen, ta ce yanzu ne lokacin daukar mataki. Shirin da aka yi wa lakabi da ''Next Generation EU'' zai kasance mafitar da ake nema inji von der Leyen. Kimanin yuro biliyan dubu daya ne dai tsarin ya kunsa, wanda ke shirin dawowa da al'amuran yau da kullum da suka shafi tattalin arziki daga shekarar 2021 zuwa 2027 ga kasashen na EU, wadanda yanzu hakan ke fuskantar barazanar durkushewa.

 Italiya da Spaniya na sahun gaba a kasashen Turai da ke bukatar wannan taimakon ganin irin ta'adin da annobar ta yi wa kasashen biyu na rayuka da dukiya. Sai dai inda gizo ke saka, shi ne ana bukatar amincewar kasashe ashirin da bakwai mambobin kungiyar kafin a aiwatar da shirin. Sai dai tuni masu lura da al'amura ke nuna fargaba kan sabon tsarin.