1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU: Takunkumi ga masu hannu a harin Siriya

Ramatu Garba Baba LMJ
April 16, 2018

Ministocin harkokin waje na kungiyar Tarayyar Turai sun soma zaman taron tattauna rikicin kasar Siriya a a kasar Luxembourg.

https://p.dw.com/p/2w9Pe
Luxemburg EU-Außenministertreffen
Taron ministocin kasashen waje na kasashen kungiyar Tarayyar Turai EUHoto: Reuters/E. Dunand

Taron ya mayar da hankali kan takaddamar amfani da makami mai guba a yankin Douma na kasar Siriya, da kuma sababbin matakan aza takunkumi kan wadanda ake zargi da hannu a al'amarin da ya salwantar da rayukan mutane da dama. Taron dai na zuwa ne bayan da Birtaniya da Faransa karkashin jagoranci Amirka suka kaddamar da hari a Siriya da zummar lallata sansanin da aka ajiye tarin makami masu guba. Amirka da ta jagoranci harin kuwa, ta ce matakin martani ne ga duk wani kokari na sake kai irin wannan hari a nan gaba. Birtaniya da ake kallon ta amsa kiran Amirka ne a kai harin, ta musanta zargin cewa tursasa ta aka yi ta dauki matakin da ake kallo a matsayin yunkurin kawar da Shugaba Bashar al-Assad na Siriyan daga karagar mulki, sai dai ministan harkokin wajen kasar Boris Johnson ya kawar da wannan tunani:

Syrien Krieg - Damaskus nach Angriff durch die USA, Frankreich & Großbritannien | Scientific Research Centre
Cibiyar gudanar da binciken kimiyya ta Siriya da harin Amirka da kawayenta ya ruguzaHoto: Reuters/O. Sanadiki

Sanya takunkumi ga masu hannu a harin

Wakilan kasashe mambobin kungiyar da ke zaman taron kuwa, sun nemi a dauki matakin aza takunkumi ga wadanda ake zargi da laifin harin makami mai gubar, matakin da ya shafi Rasha babbar aminiyar gwamnatin Assad, sai dai tuni mahukuntan Rashan suka dangana lamarin da bita da kullin siyasa suna mai cewa matakin bai da dangantaka da halin da ake ciki a Siriya ko wata kasa ta duniya face salon siyasa na gurgunta dama sauya alkiblar kasuwancin daga Rashan.

A mako mai zuwa, kungiyar ta EU za ta kaddamar da asusun samar da tallafi ga Siriya, sai dai da dama daga cikin mambobin kungiyar sun ce a yayin da hakan ke gudana dole shugaba Assad ya sauka daga mulki don kuwa ba za su bar shugaban da ya zalunci al'ummarsa ta hanyar kashe su da makamai masu guba ya ci gaba da mulki a yayin da ake kokarin samar da mafita daga rikicin kasar ba, kamar yadda ministan harkokin kasashen ketare na Jamus da ya wakilci kasar a taron na Luxembourg Heiko Maas ya nunar.