1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU ta yi tir da kalaman Erdogang kan Macron

Abdul-raheem Hassan
October 25, 2020

Babban jami'in harkokin ketare na kungiyar Tarayyar Turai Josep Borrell ya ce ba za su lamunci kalaman Shugaba Turkiyya Reccep Tayyip Erdogan na cewa Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya binciki lafiyar kwakwalwarsa.

https://p.dw.com/p/3kQHY
EU I Sanktionen gegen Russland I Josep Borrell
Hoto: Jean-Christophe Verhaegen/AP/picture-alliance

A wani sakon Twitter Borell ya bukaci shugaban Turkiyya da ya janye kalaman da ya kira masu hatsari. Sai dai Erdogan ya ya sabunta kalaman kwana guda bayan da Faransa ta janye jakadanta a birnin Santanbul.

Kasashen Faransa da Turkiyya suna rikici kan batutuwa da suka hada da iko kan albarkatun ruwa a gabashin tekun Baharrum da kuma rigingimun Libiya da Siriya da kuma na baya.-bayannan rikicin Aremeniya da Azerbaijan kan yankin Nagorno-Karabakh.