1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU ta yi barazanar katse hulda da Burundi

Salissou BoukariFebruary 15, 2016

Ministoci 28 na harkokin waje na Kungiyar Tarayyar Turai sun amince da wani kundi na shirin daukan matakai kan Burundi sakamakon rikicin siyasa da take Fama da shi.

https://p.dw.com/p/1HvgL
Hoto: picture-alliance/AP Photo/V. Mayo

Kungiyar Tarayyar Turai ta sanar da aniyarta ta daukan matakan da suka dace kan kasar Burundi a wani mataki na bada amsa ga tashe-tashen hankulan da ke gudana a kasar. Ana ganin cewar matakan za su hada da ka katsewar duk wata gudunmawa da kungiyar ke bayarwa ga kasar ta Burundi.

Ministocin harkokin wajen kungiyar ne dai guda 28 suka sanar da wannan labari a wannan Litinin cikin wani kundi da suka amince da shi wanda kuma za' a kara tabbatar da shi ya zuwa karshen watan nan ta Fabirairu. Kungiyar ta Tarayyar Turai da ke a matsayin ta kan gaba wajen tallafa wa kasar ta Burundi na shirin katse duk wata hulda da ita tare da dakatar da tallafin da take bayarwa wanda na shekara ta 2015 zuwa 2020 suka tashi miliyan 430 na Euro.