1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU ta soki gwamnatin Siriya

July 9, 2011

Ƙungiyar Tarayyar Turai ta soki matakan murƙushe masu neman kafa demokraɗiyya a ƙasar Siriya

https://p.dw.com/p/11s4Q
Kantomar harkokin ƙetare ta ƙungiyar EU Catherine Ashton.Hoto: AP

Kantomar harkokin ƙetare ta ƙungiyar EU Katharin Ashton, ta soki matakan da gwamnatin Siriya ke ɗauka na kawar da masu bore, inda tace matakan sun rage hallascin gwamnatin shugaba al-Assad. Ashton ta buƙaci gwamnatin a Damascus da ta bar masu bincike daga ƙetare su binciki lamarin, kana ta buɗe ƙarin ƙofofin tattaunawa. An ruwaito cewa jami'an tsaro sun harbe masu bore kimanin 13 a jiya. Masu fafutuka sukace aƙalla mutane rabin miliyan suka shiga boren a birnin Hama, inda jakadun Amirka da na Faransa a ƙasar ta Siriya suka ziyarci birnin domin marawa masu boren baya. Abinda gwamnatin Siriya tace hakan ya nuna ƙarara cewa, turawan yamma ne ke ruruta wutar rikicin.

Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Abdullahi Tanko Bala