1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU ta shirya kara wa Ukraine karfin yaki

October 17, 2022

Taron ministocin kasashen waje na Tarayyar Turai, ya amince da bai wa Ukraine karin kudade da ma fara wani aikin ba da horo ga sojojin kasar a yakin da take yi da Rasha.

https://p.dw.com/p/4IIdY
Ministar harkokin wajen Jamus, Annalena Baerbock a taron Luxemburg
Hoto: Bernd Riegert/DW

A taron da suka yi a kasar Luxemberg da ranar yau, ministocin kasashen ketare na kasashen na EU sun amince da karin Euro miliyan 500 don samun makamai a yakin da Ukraine ke yi da Rasha.

Kudaden da Tarayyar Turan ta taimaka wa Ukraine a bangaren sayen makaman, sun karu zuwa Euro biliyan uku da dubu dari daya.

Jamus ta yi alkawarin zama a sahun gaba wajen kara wa dakarun Ukraine din dabarun yaki.

Ministocin sun kuma sanya takunkumai a kan wasu jami'an kasar Iran wadanda ake zargi da afka wa masu zanga-zanga.

Masu bore a Iran dai na yin tir ne da mutuwar da matashiya Mahsa Amini ta yi a hannun jami'an tabbatar da da'a saboda bijire wa Hijabi.

Takunkuman da suka shafi jami'ai 15, sun hada da rufe asusun ajiyarsu da ma haramta musu takardun izinin shiga cikin kasashen na EU.