1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU ta nuna jin daɗi da samun kyautar Nobel

October 12, 2012

Wakilan tarayyar Turai sun nuna farin ciki tare da yin alfahiri da kuma mamakin samun kyautar zaman lafiya ta wannan shekara.

https://p.dw.com/p/16PN0
Hoto: Reuters

Shugabannin ƙungiyar tarayyar Turai EU sun nuna farin cikinsu da kyautar Nobel ta zaman lafiya da aka ba wa ƙungiyar a bana, a dangane da rawar da taka wajen wanzuwar zaman lafiya, sasantawa da kuma ci-gaban demokraɗiyya a nahiyar Turai. Kwamitin ba da kyautar ta Nobel dake birnin Oslo na ƙasar Norway ya ce EU ta taimaka Turai ta fita daga wata nahiya ta yaƙi zuwa wata nahiya ta wanzuwar zaman lafiya.

Bayan shekaru da yawa na yaƙe yaƙe a Turai, ƙungiyar tarayyar Turai da sauran ƙungiyoyin da aka kafa gabaninta dake da manufar haɗe kan ƙasashen Turai ta taka rawar gani wajen wanzuwar zaman lafiya, sulhu, ci-gaban demokraɗiyya da kare haƙƙin bil Adama a Turai, inji kwamitin ba da kyautar Nobel a cikin hujjar da ya bayar ta ba wa tarayyar Turan kyautar zaman lafiya ta shekarar 2012. Daga jin sanarwar ba da kyautar kuwa shugabannin EU a birnin Brussels suka fara kiran tarukan manema labaru.

Kyautar ta sosa rai a Brussels

A martanin farko da ya mayar shugaban hukumar tarayyar Turai Jose Manuel Barroso ya ce labarin ba wa EU kyautar wani abu ne da ya sosa masa rai matuƙa.

"Babbar girmamawa ce ga ƙungiyar tarayyar Turai da ta samu kyautar zaman lafiya ta 2012. Ba shakka wannan babbar girmamawa ce ga al'ummar ƙasashen Turai su miliyan ɗari biyar, da ma ƙasashe membobinta da al'ummomin ƙungiyar tarayyar Turai. Ta gaskata amincewa da irin ayyuka masu amfani da take wa al'ummarta da ma duniya baki ɗaya."

Shi ma shugaban majalisar zartaswar ƙungiyar Herman Van Rompuy ya ce lambar yabon abin alfahari ne na yaba wa ƙoƙarin ƙungiyar na tabbatar da zaman lafiya a Turai.

Finnland EU Norwegen Friedensnobelpreis 2012 an EU Herman Van Rompuy in Helsinki
"Na yi alfahari da kyautar"-Herman Van RompuyHoto: Reuters

"Mun yi yaƙi da juna shekaru aru aru. Mun yi yaƙi duniya guda biyu da suka zama wani yaƙin basasa a Turai. Mun kawo ƙarshensu. Da taimakon EU ba za a sake ganin wannan yaƙi ba. Saboda haka EU ce hukumar samar da zaman lafiya mafi girma da ba a taɓa samu ba a tarihin duniya."

Ita kuwa shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel wadda ƙasarta ke taka muhimmiyar rawa wajen haɗin kan Turai cewa ta yi kyautar za ta ƙara ƙarfafa musu guiwa don ci-gaba da namijin aikin da suke yi.

Griechenland Angela Merkel in Athen
"Za mu ƙara zage damtse"-Angela MerkelHoto: Reuters

"Ganin cewa kwamitin kyautar Nobel ya girmama wannan aiki da muke yi, hakan zai ba mu ƙwazo da ƙarin nauyi a lokaci guda musamman ma a gare ni."

Barkwanci na watan Afrilu da ya makara

Sai dai ba kowa ne ya yi maraba da kyautar ba. Alal misali 'yan Birtaniya dake sukar lamirin Turai a majalisar dokokin Turai ba'a ma suka yi da cewa irin barkwancin nan ne na watan Afrilu da ya makara. Suka ce ai a cikin shekaru biyun da suka wuce EU ta ƙirƙiro da wani yanayi na mummunar gaba tsakanin ƙasashen arewaci da kudancin Turai. Hasali ma manufar haɗewar Turan ta ruguje.

Mawallafa: Christoph Hasselbach / Mohammad Nasiru Awal
Edita: Usman Shehu Usman