1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ilham Tohti ya samu babbar lambar yabo daga EU

Abdul-raheem Hassan
October 24, 2019

Kungiyar Tarayyar Turai ta ba wa Tohti lamyar yabo ta koluluwa na kare hakkin dan adam kan rawar da ya taka na kare al'ummar Uighur marasa rinjaye a kasar China.

https://p.dw.com/p/3RrgK
Uigure Regimekritiker lebenslange Haft China Ilham Tohti
Hoto: picture-allianceAP Photo/Andy Wong

A wani mataki na cigaba da matsin lamba ga gwamnatin China kan wani dan fafitika da ke tsare a gidan yari, kungiyar EU ta kuma bukaci gwamnatin Beijin da ta gaggauta sako dan fafitikar daga yari.

A shekarar 2014 ne gwamnatin China ta kama Ilham Tohti kan yadda yake caccakar tsarinta kan al'ummar Xinjian da ke Arewa maso yammacin kasar, an kuma yanke masa hukuncin daurin rai da rai.