1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Horas da sojojin Ukraine dabarun yaki

Binta Aliyu Zurmi
February 1, 2023

Shugabannin kungiyar tarayar Turai sun sanar a wannan Laraba za su rubanya yawan sojojin kasar Ukraine da suke horas da su dabarun yaki.

https://p.dw.com/p/4MzUF
Belgien, Brüssel | EU Gipfel
Hoto: Olivier Matthys/AP/picture alliance

Shirin horas da sojoji na Ukraine da aka fara shi a watan Nuwamba shekarar bara, yanzu kasashen EU 27 sun kara yawan sojojin daga dubu 15 zuwa dubu 30, wadanda za a rarabasu a tsakanin mambobin kungiyar.

A hukumance kungiyar ta ce ya zuwa wannan Juma'ar da ke tafe za su sanar wa mahukuntan na Kyiv da wannan karin a babban taronsu.

Kasashen Amirka da Birtaniya da ma wasu da ke goyawa Ukraine din baya sun jima suna koyar da dakarun na Ukraine yadda za su sarrafa makaman da suka taimaka musu a yakin da suke ci gaba da gwabzawa da Rasha.

Dama dai Ukraine ta jima tana neman kasashen na EU da su kara yawan sojojin ta da suke horas wa. a fatan yin nasara a wannan yakin da ke dab da cika shekara guda.