1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU ta kakaba wa Rasha sabbin takunkumai

June 22, 2023

Kungiyar Tarayyar Turai ta sake amincewa da wasu sabbin takunkumai karo na 11 a kan Rasha saboda afka wa Ukraine da ta yi da yaki yau sama da shekara guda.

https://p.dw.com/p/4Suni
Ursula Von der Leyen
Hoto: John Thys/AFP

Daga cikin sabbin takunkuman da kungiyar Tarayyar Turan ta sanar a kan Rasha, sun hada da haramta zirga-zirgar musamman ta abinci da sauran kayayyakin fasaha da sojojin Rasha ke amfani da su.

Haka ma akwai haramta sayar wa da wasu kayayyakin kimiyya ga wasu kasashen da ka iya bai wa Rashar, baya ga fadada matakai kan duk wani abu da ma'aikatar tsaro ta Rasha ka amfani da shi a yakin.

Kasar Sweden din ta ce kungiyar Tarayyar Turan ta amince da sabbin takunkuman ne,a lokacin taro da ta yi a Brussels babban birnin kasar Belgium.

Tuni ma dai shugabar hukumar Turai Ursula von der Leyen, ta yi marhabin da wadannan sabbin takunkumai.