1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU ta gargadi Moscow kan daukar sojin wucin gadi

Binta Aliyu Zurmi
September 21, 2022

Kasashe mambobin Kungiyar tarayyar Turai na ci gaba da tafka mahawara bisa sabon matakin da Rasha ke shirin dauka na samar da dubban sojojin wucin gadi.

https://p.dw.com/p/4HAeq
Peter Stano I  Sprecher der Europäischen Kommission für Außen- und Sicherheitspolitik
Hoto: Dursun Aydemir/AA/picture alliance

Shugabannin na Kungiyar EU sun yi kakkausar suka tare da aike wa Moscow da sakon gargadi da ke nuni da girman sakamakon da ka iya biyo bayan sabon matakinta na tura sojoji fagen daga.

A cewar mai magana da yawun EU kan manufofin harkokin waje Peter Stano, suna ci gaba da duba irin ta'asar da Rasha ke yi a Ukraine, na baya-bayan nan shi ne batun manyan ramuka da aka gano gawawakin daruruwan fararen hula gami da na wasu sojoji da suka yi batan dabo. 

Ya zuwa yanzu babu tabbacin karin wasu takunkumai a kan Rasha bisa wannan sabon matakin amma dai Mista Stano ya ce, suna ci gaba da yin nazari kan matakan da ya dace su dauka.