1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU ta gargadi masu kasuwar bayi a Libiya

Yusuf Bala Nayaya
November 23, 2017

Tun bayan da kafar yada labaran CNN ta fitar da hoton bidiyo kan yadda ake wannan ta'asa ta cinikin bayi da 'yan Afirka bakar fata a hannun Larabawa a Libiya lamarin ya jawo suka tsakanin kasa da kasa.

https://p.dw.com/p/2oA7E
Libyen Tripoli Migrant nach Rettung durch Küstenwache
Hoto: Reuters/A. Jadallah

Kungiyar Tarayyar Turai ta bayyana a wannan rana ta Alhamis cewa za ta yi aiki tukuru wajen ganin an samu mafita kan matsalar da 'yan gudun hijira suke ciki a Libiya, inda ita ma ke da ra'ayi na Shugaba Emmanuel Macron da ya nuna bacin ransa kan gudanar da kasuwancin bayi a wannan kasa.

Tun bayan da kafar yada labaran CNN ta fitar da hoton bidiyo kan yadda ake wannan ta'asa ta cinikin bayi da 'yan Afirka bakar fata a hannun Larabawa a Libiya lamarin ya jawo suka tsakanin kasa da kasa. Kwamishinan da ke lura da harkokin 'yan gudun hijira a Kungiyar ta EU Dimitris Avramopoulos ya fadawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa tamkar abin da Shugaba Macron ke fadi ne wato sanya mutane a kasuwa babban laifi ne ga dan Adam. Ya ce suna jin abin da ke faruwa a Libiya kan 'yan gudun hijirar kuma ba za a bari ba ya ci gaba da faruwa.