1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU ta dakatar da tallafin ga Nijar

July 29, 2023

Kungiyar Tarrayar Turai ta yi watsi da juyin mulkin da sojoji suka yi a Jamhuriyar Nijar. Kungiyar ta ce Shugaba Mohamed Bazoum ne ta sani a matsayin shugaban kasar ta Nijar.

https://p.dw.com/p/4UXWZ
Hoto: Kay Nietfeld/dpa/picture alliance

A cikin sanarwar da babban jami'in harkokin waje na kungiyar Joseph Borell ya fitar, ya ce EU ta janye dukannin wani tallafi da take bai wa kasar nan take, sannan an dakatar da ayyukan hadin gwiwa ta fuskar tsaro har sai baba ta gani.

Da ma dai kungiyar ta EU ta ware dala miliyan 503 domin inganta sha'anin mulki da na ilimin kasar Nijar daga shekarar 2021 zuwa 2024.

A share guda, ita ma kungiyar Tarrayar Afirka AU ta bai wa dakarun sojin Nijar wa'adin kwanaki 15 da su koma sansanoninsu kana su mayar da kasar kan tafarkin dimukuradiyya.

A cikin sanarwar bayan taron da ta gudanar kan juyin mulkin da sojoji suka yi a Nijar, kwamittin tabbatar da zaman lafiya da sulhu a kungiyar ya bukaci sojojin su bi umurnin da ya bayar ba tare da wani sharadi ba.

Jamhuriyar Nijar ta fuskanci juyin mulki inda Janar Abdourahmane Tchiani ya ayyana kansa a matsayin shugaban majalisar soji da ke mulki a kasar a jiya, bayan hambarar da mulkin farar hula na shugaba Mohamed Bazoum.