EU ta bukaci a kwantar da hankali a Bangladesh
August 6, 2024Amurka ta jinjina wa sojojin kasar saboda yadda suka kuduri aniyar samar da gwamnatin rikon kwarya ba tare da ci gaba da kai samame kan masu zanga-zanga ba. Kungiyar Tarayyar Turai ta ce akwai bukatar kafa gwamnatin rikon kwarya bisa la'akari da mutunta hakkin dan Adam da tanade-tanade na dimukuradiyya. MDD ana ta bangare ta bukaci a gudanar da bincike mai zaman kansa a game da yadda zanga-zanga ta rikide ta koma tashin hankali har ta yi awon gaba da gwamnatin Sheikh Hasina.
Hakan na zuwa ne yayin da kungiyar daliban kasar wadda tun farko ta jagoranci zanga-zanga don nuna adawa da zargin rashin adalci wajen daukar aikin gwamnati, ta bukaci a nada wani wanda ya taba lashe kyautar lambar yabo ta zaman lafiya ta Nobel Dr Mohammad Yunus a matsayin jagoran gwamnatin rikon kwarya.
Tuni dai sojojin kasar suka sanar da matakan da suke bi wajen samar da gwamnatin ta rikon kwarya