1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU na tattaunawa kan rikicin Libiya

Ahmed Salisu
January 20, 2020

Ministocin harkokin wajen na kasashen Kungiyar EU na wani zama na musamman don tattaunawa kan hanyoyin da za a bi wajen warware rikicin kasar Libiya da ya ki ci ya kuma ki cinyewa.

https://p.dw.com/p/3WUJv
Konflikt in Libyen | Kämpfe
Hoto: picture-alliance/dpa/A. Salahuddien

Guda daga cikin abinda zaman nasu ke mayar da hankali shi ne farfado da sintiri na sojojin kungiyar a Tekun Bahar Rum da nufin tabbatar da cewar an dakile shigar da makamai ga bangarorin da ke rikici da juna.

Ministocin har wa yau za su tabo batun zaman da aka yi kan rikicin na Libiya a jiya a birnin Berlin na nan Jamus, inda ake sa ran za su bada cikakken gyoyon bayansu ga abin da taron ya cimma.

Gabannin kammala wannan zama dai, tuni wasu daga cikin kasashen na EU suka bada goyoyn bayansu ga wannan aiki wanda suke ganin zai taimaka wajen kawo karshen halin dardar da ake ciki a wasu yankuna na gabas ta tsakiya.