1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU na shirin hana 'yan Rasha shiga cikinta

August 29, 2022

Taron ministocin kasashen ketare na kungiyar EU a Jamhuriyar Czech, na duba yiwuwar hana 'yan Rasha izinin shiga kasashen da bai wa sojojin Ukraine horo.

https://p.dw.com/p/4GALo
Josep Borrell
Hoto: Olivier Matthys/AP/picture alliance

Shiri ne dai na musamman da aka bijiro da shi da nufin nazari kan kiraye-kirayen da ake yi na kasashen Tarayyar ta Turai su dauki mataki na bai daya da zai hana 'yan kasar Rasha takardun izinin shiga cikin su da sunan yawon shakatawa.

An dai dauki lokaci galibin kasashen Tarayyar Turan na bai wa sojojin kasar Ukraine horo kan yadda za su iya sarrafa makaman kasashen yamma da ake kai musu domin kare kansu daga hare-haren da Rasha ke kaddamarwa kan kasar tun cikin watan Fabrairu.

Yayin ma wani taro na hadin gwiwa a gefe guda, wakilan Majalisar Dinkin Duniya da na kungiyar tsaro ta NATO da wasu ministocin tsaron, za su tattauna kan batun dakatar da aikin kiyaye zaman lafiya da dakarun kungiyar EU da na MDD ke yi a Mali.