1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU na duba yiwuwar sake tallafawa Girka

May 10, 2011

Ƙungiyar Tarayyar Turai na nazarin matakan garanbawul na kasar Girka yayinda ƙasar ke neman tallafin tattalin arziki a karo na biyu.

https://p.dw.com/p/11DJb
Ministan kuɗin Girka George Papaconstantinou.Hoto: dapd

Manyan jami'an ƙungiyar Tarayyar Turai dake taro a Strasbourg suna duba yiwuwar ko za'a baiwa ƙasar Girka tallafin biliyoyin kuɗi a karo na biyu domin ceto tattalin arzikin ƙasar daga durƙushewa. A na ta ɓangaren Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel wadda ke ɗari-ɗari da tallafin ta baiyana cewa ba za ta ce komai akan batun ba har sai ƙungiyar EU da asusun bada lamuni na duniya IMF sun tabbatar da cewa ƙasar ta Girka ta aiwatar da alƙawuran da ta ɗauka na sharaɗin euro miliyan dubu 110 da aka tallafa mata da su a bara. Hakazalika jami'an ƙungiyar Tarayyar Turan suna kuma tattauna ƙa'idojin bashin euro miliyan dubu 78 ga ƙasar Portugal. Wajibi ne ga ƙasar ta Portugal ta ɗauki tsauraran matakan tsimi waɗanda suka haɗa da yin garanbawul ga harkokinta na kasuwannin kuɗaɗe da magance kaucewa haraji da kuma sayar da hannun jarin gwamnati a manyan kamfanoni.

Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita: Ahmad Tijani Lawal