1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU: Kokarin hana fidda man Rasha zuwa waje

Binta Aliyu Zurmi
March 6, 2022

Amirka da kasashen EU za su dakatar da amfani da duk wani makamashi da suke shigar wa kasashensu daga Rasha a kokarin ci gaba da ladabtar da kasar kan mamayar da take yi wa Ukraine.

https://p.dw.com/p/4865W
Symbolbild | Nigeria Gaspipeline
Hoto: Florian Plaucheur/AFP/Getty Images

Kasar Amirka da takwarorinta na kasashen Turai na duba hanyoyin dakatar da shigar da makamashin iskar gas da na fetur cikin kasashensu daga Rasha.

Sai dai a yayin da suke kokarin daukar wannan matakin, sakataren harkokin wajen Amirka Anthony Blinken ya ce akwai bukatar tabbatar da duniya na ci gaba da samun isashen mai wanda ke da matukar mahimmanci.

Wannan dai na zuwa ne a lokacin da farashin mai a ko'ina a fadin duniya ya yi tashi gwauron zabi a sabili da wannan yaki na Rasha.

Yanzu haka dai mista Blinken da ke ziyarar aiki a nahiyar Turai na kokarin shawo kan shugabannin nahiyar don zama tsintsiya madaurinki daya.

Amirka na shigar da kaso 8 cikin 100 na adadin man da take amfani da shi a kowane wata daga kasar Rasha.