1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU da AU sun damu kan halin tsaron Bazoum

Mouhamadou Awal Balarabe
August 11, 2023

Kungiyar Tarayyar Turai da takwarta ta Afirka sun bayyana matukar damuwa kan tabarbarewar yanayin ake ci gaba da tsare hambararren shugaban Nijar Mohamed Bazoum da iyalansa tun bayan juyin mulkin 26 ga watan Yuli 2023.

https://p.dw.com/p/4V322
Hambararren shugaban Jamhuriyar Nijar Mohamed Bazoum da sojoji suka tsareHoto: Ludovic Marin/AFP

Kantoman harkokin wajen EU Josep Borrell ya ce gwamnatin mulkin sojan Nijar ta hana Bazoum da danginsa abinci tare da katse musu wutar lantarki tun kwanakin da suka wuce. Shi kuwa Shugaban Kungiyar Tarayyar Afirka Moussa Faki Mahamat ya ce ba za su amince da duk nau'i da wulakanci da hukumomin sojin Nijar ke nuna wa Shugaba Bazoum ba. Sannan ya bayyana cikakken goyon bayansa ga matakin ECOWAS/CEDEAO na turawa da sojoji don maido da tsarin dimokuradiyya a Nijar.

A Nata bangaren kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch wacce ta zanta da Shugaba Bazoum, ta bayyana rashin mutuntawa da rashin tausayi da ake nuna wa Bazoum. Ita dai Kungiyar ECOWAS tana fatan ganin an warware rikicin na Nijar cikin lumana, ko kuma ta yi amfani da karfin bindiga wajen kwato mulki daga hannun sojoji kasar.