1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU ta cimma yarjejeniya kan riga-kafin corona

November 10, 2020

Hukumar zartaswa ta Tarayyar Turai za ta samar da allurar riga-kafin cutar corona bayan da aka tabbatar da ingancinsa da kamfanonin BioNTech da Pfizer su ka yi.

https://p.dw.com/p/3l7AD
Symbolbild Corona Impfstoff Biontech und Pfizer BNT162bt
Hoto: Jens Krick/Flashpic/picture alliance

Shugabar Hukumar Ursula von der Leyen ta ce hukumar za ta tabbatar da yarjejeniyar a ranar Laraba baya aiki tukuru da ta yi don tabbatar da yiwuwar samun maganin riga-kafin a watannin da suka gabata. Kamfanin hada magungunan na Pfizer dai ya ce sakamakon gwajin farko na riga-kafin na da ingancin da zai yi tasiri ga cutar da kashi 90.

Tuni ma dai hukumar zartaswar ta Tarayyar Turai ta riga ta kulla wasu yarjejeniya tare da kamfanonin hada magunguna da zai bai wa mambobinta 27 damar sayen allurai na yiwuwar riga-kafin coronavirus kimanin biliyan daya.