1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU: Bukatar hana shawagin jiragen sama a arewacin Siriya

Abdullahi Tanko Bala
March 5, 2020

Babban jami'in harkokin wajen kungiyar tarayyar Turai Joseph Borrel ya ce ya kamata NATO ko Majalisar Dinkin Duniya su shata da'irar hana shawagin jiragen sama a arewa maso yammacin Siriya

https://p.dw.com/p/3YvtW
Türkei Tränengaseinsatz gegen Flüchtlinge an der Grenze zu Griechenland
Hoto: picture-alliance/AA/H. M. Sahin

Ministocin harkokin waje na kungiyar tarayyar Turai EU sun gudanar da taro a wannan Alhami din a Zagreb domin tattauna halin da ake ciki musamman batun 'yan gudun hijira a kan iyaka tsakanin Turkiyya da kasar Girka da kuma yanayin da lardin Idlib na Siriya yake ciki.

Ministan harkokin wajen Croatia Gordan Grlic Radman da babban jami'in harkokin wajen tarayyar Turai Joseph Borrel suka karbi bakuncin taron.

A yayin tattaunawar Borrel ya baiyana goyon baya ga bukatar Turkiyya na shata wata da'ira ta hana shawagin jiragen sama a arewa maso yammacin Siriya.

Sai dai yace ya rage ga kungiyoyi kamar NATO da Majalisar Dinkin Duniya su shata da'irar hana shawagin jiragen saman.

A waje guda shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi kiran samar da wani yanki na tsaro domin kare fararen hula.