1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU na binciken aikata laifin cin hanci da rashuuwa

Abdoulaye Mamane Amadou Lateefa Mustapha Jaafar
December 11, 2022

An sauke mataimakiyar shugabar majalisar dokokin Turai 'yar kasar Girka Eva Kaili daga mukaminta, bisa zargin badakalar cin hanci da hukumomin Beljiyam suka bankado.

https://p.dw.com/p/4Kmug
Eva Kaili
Eva Kaili mataimakiyar shugabar majalisar dokokin kungiyar EUHoto: Eric Vidal/AFP

Alkali mai shigar da kara a Beljiyam na tuhumar matar 'yar Girka Eva Kaili, da karbar cin hanci daga Qatar, wacce ke karbar bakwancin gasar cin kofin duniya a yanzu haka, kana da amfani da matar don samun goyon bayan majalisar dokokin nahiyar Turai ta hanyar biyan wasu kudade kai tsaye ko kuma ba da na goro.

Mme Kaili na daga cikin mutane biyar da hukumomin Beljiyam suka cabke a wannan Jumma'a, bayan da suka kaddamar da bincike, to amma za ta ci gaba da karba sunan mukaminta har sai bayan majalisar dokokin ta EU ta kada kuri'ar tsigeta daga mukamin.