1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Erdogan ya sha alwashi kan mutuwar Morsi

Zulaiha Abubakar
June 20, 2019

Shugaba Receep Tayyip Erdogan na Turkiyya ya dauki alwashin bin diddigin mutuwar tsohon shugaban kasar Masar Mohammed Morsi. Wannan ya zo ne bayan da Masar ta soki Erdogan bayan wasu kalamai kan mutuwar Morsi.

https://p.dw.com/p/3KlWr
Türkei | Neuwahlen Istanbul | Wahlkampf | Erdogan
Hoto: picture-alliance/Presidential Press Service via AP

Erdogan ya  kara da bayyana tabbacin kashe tsohon shugaban aka yi kamar yadda ta faru kan dan jaridan nan Jamal Kashoggi. Erdogan ya jima yana bayyana tsananin adawarsa ga shugabancin Abdel-Fattah el-Sisina Masar. Tuni dai ma'aikatar harkokin kasashen wajen kasar ta Masar ta bayyana cewar irin wadannan kalamai na Erdogan sun kara tabbatar da alakarsa da kungiyar 'yan uwa Musulmi wacce gwamnatin Masar ta jima da ayyanawa a matsayin kungiyar 'yan ta'adda.

A ranar Litinin ce dai Muhammed Morsi ya yanke jiki ya fadi a kotu, al'amarin da ya sanya kungiyoyin kare hakkin 'dan Adam dora alhakin mutuwarsa kan gwamnatin Masar sakamakon yadda ta yi watsi da bukatar mamacin na kula da lafiyarsa a gidan kurkuku.