1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turkiya: Erdogan ya janye karar yarfe

Lateefa Mustapha Ja'afarJuly 30, 2016

Shugaban kasar Turkiya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana janye duk wata kara da ya shigar da ta shafi yarfen siyasa ko kuma kagen da yake zargin an masa.

https://p.dw.com/p/1JYpt
Türkei Erdogan
Hoto: picture-alliance/AA/A. Izgi

Erdogan ya bayyana wannan mataki da ya dauka da cewar wata alama ce mai kyau. A watannin baya-bayan nan dai ministan shari'a na kasar ta Turkiya ya nunar da cewa akalla akwai irin wadannan kararraki da suke jiran shari'a 1,800 wadanda kuma suka shafi wasu 'yan adawa a kasar. Babu tabbaci kan cewa ko kararrakin da Erdogan ya janye sun hadar da wadanda yake zargin 'yan kasashen ketare da cin zarafin nasa, misali mawakin barkwancin nan na Jamus Jan Böhmermann da ya yi waka a kan yanayin mulkin Erdogan din a baya-bayan nan. A jawabin da ya yi a fadar mulkinsa da ke Ankara, Erdogan ya zargi kasashen yamma da marawa 'yan tawayen kasar baya, inda ya ce babu wani wakili da Amirka ko kuma kungiyar Tarayyar Turai wato EU suka tura zuwa Turkiya domin ya yi masa jaje, sakamakon yunkurin juyin mulki da ya fuskanta a farkon wannan wata na Yuli da muke ciki.