1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turkiyya: Ko Erdogan zai yi tazarce?

Lateefa Mustapha Ja'afar
May 14, 2023

Sakamakon farko na kuri'un da aka kidaya bayan kammala zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun dokoki a Turkiyya, na nuni da cewa Shugaba Recep Tayyip Erdogan na kan gaba.

https://p.dw.com/p/4RLAo
Turkiyya |  Zabe | Kidayar Kuri'u
Ci gaba da kidaya kuri'u bayan zaben shugaban kasa da na 'yan majalisu a TurkiyyaHoto: Emilie Madi/REUTERS

Kamfanin dillancin labaran Turkiyyan Anadolu ya ruwaito cewa a kaso 47 cikin 100 na kuri'un da aka kidaya, Shugaba Recep Tayyip Erdogan da ya kwashe shekaru yana mulki a Turkiyya a matsayin firaminista da kuma shugaban kasa ya samu sama da kaso 52 cikin 100.  Sai dai babban mai adawa da Shugaba Erdogan na tsawon shekaru wato Kemal Kilicdaroglu da rahotannin Anadolu din suka bayyana ya samu kaso sama da 41 cikin 100 na kuri'un da aka kidaya, ya sa kafa ya yi fatali da sakamakon yana mai cewa shi ne ke kan gaba. In har babu dan takarar da ya samu kaso 50 cikin 100 na kuri'un da aka kada bayan kammala kidaya su, za a gudanar da zagaye na biyu na zaben a ranar 28 ga wannan wata na Mayu da muke ciki.