Erdogan na ci gaba da ziyara a Afrika
December 26, 2017Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya sauka a kasar Chadi a wannan Talata a wata ziyarar kwana biyu a ci gaba da ziyarar da yake a kasashen Afrika. Daga cikin wadanda suka raka shi akwai 'yan majalisar zartaswa tara da kuma manyan 'yan kasuwar kasar. A farkon ziyarar tashi dai Erdogan ya fara ziyartar kasar Sudan inda suka kulla wata jarjejeniyar cinikayya tsakanin Sudan da Turkiyya.
Ya kuma kara da cewar Turkiyya za ta bude ofishin jakadanci a dukkanin kasashen Afrika. A nasa bangaren shugaba Omar Al-Bashir na Sudan ya bayyana farin cikinsa a kan batun bude ofishin jakadancin da Turkiyya take niyyar yi a nahiyar.
Kotun hukunta masu aikata manyan laifuka ta duniya ta bada umarnin a cafke Omar Al-Bashhir a shekara ta 2009 da kuma shekara ta 2010 a kan laifukkan da suka hada da kisan kiyashi da take hakkin 'dan Adam a yankin Darfur.
Wannan ziyarar kasashen Chadi da Sudan a Afrika ita ce irinta ta farko da shugaban kasar Turkiyya ya yi a tarihin kasar.