1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yarjejeniyar Kamaru da Equatorial Guinea

Zakari Sadou ZUD/ZMA
March 19, 2023

Kamaru ta kulla yarjejeniyar sarrafa iskar gas da kasar Équatorial Guinea, a wani mataki na farfado da tattalin arzikinta da ya samu komabaya a 'yan shekarun nan.

https://p.dw.com/p/4OuNw
Shugaban Kamaru Paul Biya
Hoto: Jemal Countess/UPI/newscom/picture alliance

Shugaban kasar Kamaru Paul Biya ne ya sanar da kulla sabuwar yarjejeniyar da takwaransa na kasar Equatorial Guinea Teodoro Obiang Nguema. Shugabannin biyu sun amince da yarjejeniyar ta  hako danyen mai da iskar gas a kan iyakokinsu yayin taron kungiyar raya tattalin arzikin kasashen tsakiyar Afirka ta CEMAC da ya gudana Juma'ar da ta gaba a birnin Yaoundé na Kamaru.

Wakilin gwamnatin Kamaru Dalvaris Ngoudjou  ya ce yarjejeniyar za ta mayar da hankali kan daidaita zuba hannun jari a bangaren iskar gas a tsakanin kasashen biyu. Ya ce a karkashin yarjejeniyar Equatorial Guinea za ta sarrafa gas din Kamaru.

 

To ko wane irin alfanu Kamaru za ta samu a wannan yarjejeniyar a daidai lokacin da hankulan kasashen yammacin duniya ya karkata kan nahiyar Afirka don neman makamashi saboda yakin Rasha da Ukraine? Masanin tattalin arziki Edmond Kuate a Kamaru ya ce matakin zai kawar da matsalolin da Kamaru ta samu bayan da gobara ta lalata kamfanin sarrafa gas na Sonara.