1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Equatorial Guinea ta rufe iyakarta da Kamaru

November 1, 2022

Equatorial Guinea ta sanar da rufe iyakokinta na tudu tun daga wannan mako domin ta kare kanta daga abin da ta kira katsalandan a yayin yakin neman zaben shugaban kasa da za a fara a wannan mako.

https://p.dw.com/p/4IuZe
Äquatorialguinea Vizepräsident Teodoro Nguema Obiang Mangue
Mataimakin shugaban kasar Equatorial Guinea Teodoro Nguema Obiang MangueHoto: Michele Spatari/AFP/Getty Images

Mataimakin shugaban kasa Teodoro Nguema Obiang Mangue bai bayyana ranar da ake sa ran sake bude iyakokin kasar da Kamaru da Gabon ba, amma ya ce za a iya ci gaba da amfani da sufurin sama wajen kulla alaka a tsakanin makwabtakan kasashen da Equatorial Guinea.

A watan Afrilun shekara mai zuwa ya kamata a gudanar da zaben  shugaban kasar, to amma gwamnatin kasar mai mutane miliyan 1.3 ta dawo da shi wannan wata na Nuwamba domin gudanar da zaben lokaci guda da na 'yan majalisar dokoki domin rage kashe kudin gudanar da zabubbukan.