Eid el Fitr: Shugaba Tinubu ya bukaci hadin kan kasa
April 10, 2024Shugaban wanda ya yi sallar Idi a Lagos ya taya dukkan musulmi murnar kammala azumin watan Ramadan tare da kira a ci gaba da addu'ar zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar baki daya.
A Jihar Kano shagulgulan sallah sun gudana lami lafiya ba tare da wani tashin hankali ba duk da hasashen da jami'an tsaro suka yi na yiwuwar samun farmaki. Mai martaba sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero da gwamnan kano Abba Kabir Yusuf sun yi sallah a babban masallacin idi na Kano da ke kofar mata.
Karin Bayani: Najeriya: An gudanar da sallar Idi cikin lumana
Duk da matsin tattalin arziki da tsadar rayuwa da ake ciki galiban mutane sun fito cikin sabbin kaya fuskokinsu cike da annashuwa ta murnar barka da arzikin ganin wannan rana bayan kamala azumi na 30 na watan Ramadana.
SC Ibrahim Abdullahi kakakin rundunar tsaro ta civil defence a Kano ya ce sun dauki matakin dakile duk wani tashin jankali inda suka sanya jami'an su na farin kaya cikin shirin ko ta kwana
Karin Bayani: Yau ta ke Sallah a kasashen musulmi
A waje guda kuma an yi hawan sallah cikin lumana Jama'a na cewa sallar bana babu korafi. Bisa al'ada a Kano bayan hawan sallah washe gari kuma za ayi hawan Daushe, a rana ta biyu kuma ayi hawan Nasarawa, wanda shine 'yan biirni ke kure adaka da kwalliya ta kece raini. Hawa na karshe da Sarkin na Kano ke a wannan sallar ita ce hawan Fanisau.