1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EFCC ta gurfanar da Dick Cheney a gaban Ƙuliya

December 8, 2010

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar Amurka na fuskatar zargin cin hanci da rashawa

https://p.dw.com/p/QTfg
Dick CheneyHoto: AP


A wani abun da ke iya sauya dangantaka tsakanin Najeriya da Amurka, hukumar da ke yaƙi da yiwa tattalin arziƙin ƙasar zagon ƙasa EFCC, ta gurfanarda tsohon mataimakin shugaban ƙasar Amuruka Dick Cheney da waɗansu mutane takwas gaban ƙuliya. Ana zarginsu ne da  laifin cin hanci da rashawa a kan abin kunyar da ya faru a kampanin Halliburton na Amurka, ko da yake awai jan aiki ga hukumar, na tuso ƙeyar tsohon mataimakin shugaban ƙasar ta Amurka zuwa Najeriya.

Mawallafi: Uwais Idris Abubakar

Edita   : Zainab Mohammed Abubakar