1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin ECOWAS na daukar matakan soja

Lateefa Mustapha Ja'afar
August 4, 2023

Shugabannin sojojin kasashen Afirka ta Yamma, sun tsara matakin yiwuwar amfani da karfin soja a kan jagororin juyin mulkin da aka gudanar a Jamhuriyar Nijar.

https://p.dw.com/p/4Unb6
Najeriya | Abuja | ECOWAS | CEDEAO | Taro | Nijar | Juyin Mulki
Shugabannin sojojin Afirka ta Yamma sun amince da tsarin daukar matakin soja a NijarHoto: KOLA SULAIMON/AFP

Shugabannin sojojin kasashen Afirka ta Yamma sun sanar da hakan ne, jim kadan bayan kammala wani taro da suka yi a Abuja fadar gwamnatin Najeriya. Kwamishinan harkokin siyasa da zaman lafiya da tsaro na kungiyar Habaka Tattalin Arzikin Kasashen Yankin Afirka ta Yamman Abdel-Fatau Musah ne ya bayyana hakan, yana mai cewa za su dauki wannan mataki in har sojojin da suka kifar da gwamnati a Nijar din ba su sauka daga kan kujerar nakin da suka hau ba.