1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ECOWAS: An dage taron manyan hafsoshin soji

Binta Aliyu Zurmi
August 12, 2023

Kungiyar ECOWAS ta sanar da dage taron manyan hafsoshin sojin kasashen yammacin Afrika da aka shirya gudanar da shi a babban birnin Accra na kasar Ghana don tattauna batun tura rundunar ko-ta-kwana Nijar.

https://p.dw.com/p/4V5d1
Nigeria Abuja | ECOWAS-Treffen zur Lage in Niger
Hoto: KOLA SULAIMON/AFP

Jagororin ECOWAS sun ce zaman taron da ka shirya gudanarwa a baya, zai duba hanyoyin da suka fi dacewa na tura dakarunsu na rundunar ko ta kwana a jamhuriyar Nijar.

To sai dai kungiyar ta ECOWAS ba ta bayyana wani kwakaran dalilin dage taron ba, kuma hakan na zuwa ne kwana guda bayan da dubban al'umma a jamhuriyar Nijar suka gudanar da zanga-zanga a gaban sansanin sojin Faransa. sun kuwar Allah wadai ga Faransa da kuma kungiyar ta ECOWAS.

Sojojin da suka kifar da gwamnatin Shugaba Mohammed Bazoum na zargin Faransa da ingiza shugabannin kasashen ECOWAS na daukar wannan tsatsauran mataki a kansu.

Kungiyar Tarayyar Afrika da takwarta ta Turai na ci gaba da bayyana matukar damuwa kan tabarbarewar yanayin da ake ci gaba da tsare hambararren shugaban na Nijar Mohamed Bazoum da iyalansa inda suka yi kira na a gagauta sakinsa.