Dussar ƙanƙara a Jamus
November 30, 2010Talla
Hukumomin kula da al ´amuran sufiri na jiragen sama sun soke tashi jirage sama 200 a filin saukar jiragen sama na birnin Francfort dake a yammacin Jamus.
Hukumomin sun ɗauki wannan mataki saboda rashin kyawan yanayin da ake cikinsa na dussar ƙanƙara da ke zuba kai a kai a Jamus
Wani kakakin hukumar filin jiragen saman ya ce za a samu jinkiri ko a nan gaba, wajan tashin jiragen, saboda aikin da ake cikinsa na kakkaɓɓe dussar ƙanƙara da ta kwanta akan jiragen.
Mawallafi: Abdurahan Hassane
Edita: Yahouza Sadissou Madobi