Dusar kankara na barazana a Turai
Hunturu ya haifar da matsaloli a wurare da yawa a kudancin Jamus, inda zubar dusar kankara ta sa hanyoyin mota da na jirage toshewa yayin da bishiyoyi suka karye. A wani bangare kuma harkar sufuri ta gurgunce.
Dusar kankara na zuba ba kakkautawa
Share gilashin mota a yanayin tsananin sanyi da zubar dusar kankara na bukatar dagewar gaske. Wadannan mutane da ke cikin wani daji na jihar Bavariya da ke kudancin Jamus sun dauki lokaci kafin haka ta cimma ruwa.
Aiki tukuru na share kankara
Ba wai kawai wurare mallakin kananan hukumomi ne ake share dusar kankarar ba - ko da masu zaman kansu ma akwai dusar mai yawa da ya kamata a tsabtace - ko kuma a rage yawanta, kamar yadda yake wakana a nan Warngau kusa da birnin Munich.
"Muna kokarin kawar da dusar kankara"
A filin jirgin saman Munich, dusar kankara ta haddasa jinkirin tashin jirage, lamarin da ke haifar da rashin jin dadi a tsakanin fasinjoji. An soke zirga-zirgar jirage 140 a karshen mako. "Muna zage dantse don ganin cewar mun kawar da dusar kankara," inji kamfanin jirangen saman Jamus wato Lufthansa.
Dusar kankara na jinkirin zuwa hutu
Bisa dalilai na rashin kyaun yanayi da zubar dusar kankara, an dakatar da tashin jirage da dama. Matakan kare jiragen sama a Munich sun sa an samar da ratar lokaci tsakanin tashi da saukar kowanne daga cikinsu. Share kankara a jikin jirgi - kamar wannan Airbus A321 - na bukatar karin lokaci.
Zirga-zirga ta tsaya cak
Kilometa 30 na cunkoso: wannan shi ne tarihin da aka kafa a kan wata babbar hanyar mota da ke jihar Bavariya. Bishiyoyi da suka fadi sun tsare hanya a garin Siegdorf. Zubar dusar kankara a kudancin Jamus ta jefa mutane cikin bala'i, kuma har yanzu akwai hadari.
Zubar kankara a tashar jirgi
Wanda ya yi tunanin cewar zai bi jirgi don zuwa wani wuri a lokacin sanyi, to ya rudi kanshi. Saboda kullum dusar kankara na zuba a hanyar da jirage ke zirga-zirga. Bishiyoyi sun karkace saboda nauyin dusar kankara da ke zuba kan layin dogo. Ana dakatar da aikin jiragen kasa kamar a wannan tasha ta Marktoberdorf a Bavariya.
Wahalar kwashe dusar kankara
Jami'an kwana-kwana, da jami'an kula da tsabta bisa taimakon sauran ma'aikata na kokarin kwashe dusar kankara da ta lullube layin dogo, kamar yadda yake faruwa a nan cikin wani daji a jihar Baden-Wuerttemberg.
Wasa a kan kankara
Idan a gefe daya dusar kankarar na cutar da wasu, amma tana faranta ran wasu: A jihar Baden-Württemberg wani Baba na jan 'ya'yanshi da babbar mota domin tayasu zamiya a kan kankara. Saboda haka ake iya zamiyar kankara ko ba a kan tsauni ba.
Gari na zama fari a lokacin sanyi
Tabbas ba abin da ya fi hoton lokacin zubar dusar kankara kyau: Baya ga kyaun yanayi, yana faranta ran wasu. Yara na jin dadi saboda a wurare da dama a kan rufe makaranta.