1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin siyasar Aljeriya ya dauki hankalin duniya

Mouhamadou Awal Balarabe
March 22, 2019

Manyan kasashen duniyya sun fara bayyana matsayinsu kan rikicin siyasa da ke barazana ga kujerar mukin shugaban Aljeriya Abdelaziz Boutefika.

https://p.dw.com/p/3FX3C
Algerien Proteste in Algier
Hoto: Reuters/Z. Bensemra

Manyan kasashen duniyya sun fara bayyana matsayinsu kan rikicin siyasa da ke barazana ga kujerar mukin shugaban Abdelaziz Boutefika. Wannan na faruwa ne sakamakon rangadin da mataimakin-Firaminista kuma ministan harkokin wajen Aljeriya Ramtane Lamamra ke yi a Rasha da Chaina da Jamus, don neman mafita ga guguwar neman sauyi da ta kada a kasar.

Gwamnatin Aljeriya na neman shawo kan manyan kasashen duniya don su ba da hadin kai ga yunkurin shugaba Abdelaziz Boutefika na tsawaita wa‘adin mukinsa da nufin gano bakin zaren warware rikicin siyasa da ake fama da shi a kasar. Saboda haka ne ministan harkokin wajen Algeria Ramtane Lamamrane ya fara ya da zango a Rasha a kan hanyarsa ta zuwa Italiya da Jamus da kuma Chaina.

Wasu masu zanga zana a birnin Algiers
Wasu masu zanga zana a birnin AlgiersHoto: Reuters/Z. Bensemra

Wasu daga cikin shugabannin adawa sun yi na’am da wannna mataki na gwamnatin Ajeriya, ciki har da Ramdane-Youssef Tazibt da kuma Seddik Chihab, kakakin jam’iyyar RND. Sai dai tsohon ministan harkokin Wajen kasar Aljeriya Ali Benflis ya nesanta kansa daga duk wani yunkuri na kasashen waje don daidaita al’amuran cikin gida.

Amurka ta yi kira ga bangarori daban- daban da su mutunta bukatun 'yan Aljeriya. Yayin da Faransa da ta yi wa kasar mulkin mallaka ta ce tana bin diddigin abin da ke faruwa a Aljeriya, amma kuma ba ta da niyyar yin shisshigi a lamuran siyasar kasar. Sai dai bayan da ya gana da takwaran aikinsa na Rasha Serguei Lavrov, ministan harkokin wajen Ajeriya Ramtane Lamamra ya ce kasarsa na bukatar kasashen waje su taimaka wa Aljeriya rubuta sabon babin siyasa.

A lokacin da guguwar neman sauyi ta kada a Aljeriya a watan da ya gabata, kasashen waje sun ta yin kaffa-kaffa wajen yin tsokaci kan abin da ke faruwa a kasar.