Dubunnan yan gudun hijira daga Siriya na kwarara Turkiyya
June 15, 2011Dubunnan al´umomin dake zaune a yankin arewacin Siriya na cigaba da tsallakawa zuwa kasashen Turkiya da Lebanan domin kauracewa kisan gillar sojojin shugaba Basahr Al-Assad.
A waje daya, magoya bayan shugaban sun shirya wani kasaittacen jerin gwano a birnin Damaskus domin shaidawa duniya cewar Assad shima ya na da masoya.
A yayin da ya ke tsokaci game da kwawarar mutanen Siriya zuwa Turkiyya ministan harakokin wajen Turkiyya, Ahmat Davutoglu cewa yayi Turkiya ba za ta rufe iyakokinta ba:
"Za mu cigaba da karbar yan gudun hijira daga Siriya, amma mu na kira ga gwamnatin Siriya ta tausaya ta daina kai hari ga jama´arta."
Daga cikin yan dugun hijirar har da sojojin da suka burjinewa gwamnati, wanda kuma suka ce a na cilasta masu ne aikata hare-hare ga fara hula
Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Ahmad Tijani Lawal