1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan gudun hijirar Sudan a Chadi na fama da yunwa

Abdourahamane Hassane
November 17, 2023

Dubban yara da suka tsere daga Sudan tare da iyayensu domin samun mafaka a kasar Chadi na cikin wani mawuyacin hali na rashin abinci mai gina jiki in ji kungiyar likitoci na kasaa da kasa MSF.

https://p.dw.com/p/4Z5lx
Hoto: dapd

Kasar Chadi wadda tuni ta karbi bakuncin mafi yawan 'yan gudun hijirar Sudan, kusan dubu 900,000, ta yi marhaban da sabbin sama da dubu takwas a makon farko na watan Nuwamba kadai. A cewar hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya.Wannan kwararowar ta kara tsananta a cikin 'yan makonnin nan daga Darfur. Lardin Sudan mai iyaka da gabashin Chadi, wurin da ake fama da tashin hankali a cewar Majalisar Dinkin Duniya, wanda a baya-bayan nan ta ce ana fargabar yiwuwar wani sabon kisan kare dangi a can.