1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dubban 'yan Ukraine sun tsallaka Poland

Abdullahi Tanko Bala
February 28, 2022

Hukumar kula da yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce kawo yanzu mutane kimanin 400,000 suka fice daga Ukraine kuma adadin na cigaba da karuwa.

https://p.dw.com/p/47hTL
Polen ukrainische Flüchtlinge an der Grenze
Hoto: Omar Marques/Getty Images

Kasar Poland ta ce mutane 100,000 suka tsallaka zuwa cikin kasarta ta kan iyaka da Ukraine yayin da wasu 50,000 suka shiga kasashen Hungary da Romania wasu dubban jama'ar kuma na kan hanyar isa Moldova. 

Mai magana da yawun hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya Joung-ah Ghedini-Williams ta ce Majalisar Dinkin Duniya na tsammanin mutane kusan miliyan hudu za su yi kaura zuwa cikin kasashe mabkwabta.

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres yace majalisar ta kudiri aniyar kara yawan taimakon jinkai ga kasar Ukraine sakamakon halin da ake ciki na mamayar da Rasha ta yi mata.

Ya shaidawa shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ta wayar tarho cewa a ranar Talata Majalisar Dinkin Duniya za ta kaddamar da gidauniya domin taimaka wa Ukraine gudanar da wasu ayyuka.