1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

DSK: saban shugaban assunun bada lamani na dunia ( IMF)

Yahouza S.MadobiSeptember 29, 2007

Taƙaittacen tarihi da ƙalubalen da ke gaban Dominique Strauss-Khan saban shugaban assusun bada lamani na dunia IMF.

https://p.dw.com/p/BvQO
Hoto: IMF

Ranar juma´a da ta wuce, membobin komitin zartaswa na assusun bada lamani na dunia wato IMF, su ka zaɓi Dominique Strauss Khan, ɗan ƙasar France a matsayin saban shugaban wannan assusu.

An haifi Dominique Strauss Khan da faransawa ke wa laƙabin DSK, ranar 25 ga watan Aprul shekara ta 1949 a ƙasar France.

Ya sami digirin digirgir, ta fannin ilimin tattali arzikin wanda har ma ya koya a babbar jami´ar birnin Paris.

Ya shiga komitin zartaswa na jam´iyar PS ta yan gurguzu, a ƙasar France a shekara ta 1983, inda daga nan ya ci daba da riƙe muƙamai daban-daban.

Alal misali, ya yi zama ministan tattalin arziki a ƙasar France.

A lokacin da a ka fara yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa a France shekara da ta gabata, ya ajje takara a jam´iyar sa ta Ps amma Segolene Royal ta kasa shi.

A watan ogust, saban shugaban ƙasar France Nikola Sarkozy , a cikin tsarin sa na damawa da jam´iyun adawa a harakokin mulki, ya gayyaci DSK, ya shiga takara a shugabanci asusun bada lamani na dunia.

Ba da wata wata ba, ya amince da wannan tayi,ya kuma ci gaba da yaƙin neman zaɓe har ranar juma´a da ta wuce.

Dominique Strauss Khan ya sami nasara da gargaramin rinjaye, a kann abokin hammayar sa, Joseph Tosovosky.

DSk ya gaji Rodrigo Rato a kujera shugabancin IMF tare da matsaloli masu tarin yawa.

To saidai ya alkawarta gudanar da kwaskwarima ta yadda assusun zai tafiya daidai da zamani.

Shugaba mai barin gado Rodrigo Rato, ya bayana wasu daga cenje-cenjen da ya cencenta a aiwatar ga IMF.

ƙasashe da kafofin kudi da dama na dunia na korafi a game da yadda asusun ke gudanar da al´amura ba tare da shawarwari ba, aceware Andrew Crocket masharahanci ta fannin tattalin arziki a jaridar JP Morgan, ya zama wajibi a sake lale.

Shima Timothy Adams, na Jaridar tattalin arzki ta Lindsey Group da ke Amurika, assusun bada lamani na dunia, nada kyaukyawar makoma,amma da sharaɗin ci gaba da saban tsarin da aka fara gudanarwa a cikin sa.