1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Donald Trump na shirin ganawa da Kim Jong Un

Abdourahamane Hassane
June 11, 2018

Shugaban Donald Trump na Amirka ya ce yana da kyakyawan fatan cewar ganawar da za su yi a gobe Talata da shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un a Singapur za ta yi armashi .

https://p.dw.com/p/2zJo6
Singapur Vor Kim Trump Gipfeltreffen | Treffen zwischen Premierminister Lee Hsien Loong und Donald Trump
Hoto: picture-alliance/dpa/Ministry of Communications and Information Singapore/MCI Photographer

Donald  trump ya bayyana haka ne a lokacin wata liyafar cin abinci da firaministan Singapur ya shirya masa. Shugaban na Amirka ya ce wannan ganawar wata dama ce ta kai wa ga cimma yarjejeniya dakatar da keran makaman nukiliya  na Koriya ta Arewa, ko da shi ke ya ce ba shi da tabbas a game da abin da tattaunawar za ta haifar.