1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

An kafa dokar hana fita a Sri Lanka

Suleiman Babayo ATB
September 22, 2024

A kasar Sri Lanka duk da zaben shugaban kasa da aka gudanar cikin kwanciyar hankali da tsanaki, an kafa dokar hana fitar dare bayan kammala zaben.

https://p.dw.com/p/4kvus
Sri Lanka Colombo | Zaben shugaban kasa
Zaben shugaban kasar Sri LankaHoto: Dinuka Liyanawatte/REUTERS

Gwamnatin kasar Sri Lanka ta kakaba dokar hana fitar dare a wannan Asabar duk da yadda aka gudanar da zaben shugaban kasa cikin tsanaki da kwanciyar hankali. Gabanin rufe runfunan zaben an samu fitowar kimanin kaso 70 cikin 100 na masu kada kuri'a. Shugaba Ranil Wickremesinghe da yake rike da madafun ikon kasar yana neman wa'adi domin tabbatar da daidaita tattalin arzikin kasar.

Wickremesinghe mai shekaru 75 da haihuwa lokacin da ya karbi ragamar mulkin kasar tattalin atzikinta ya durkushe, abin da ya haifar boren da ya tilasta wa tsohon shugaban kasar Gotabaya Rajapaksa ajiye madafun iko a shekara ta 2022.

Hukumar zaben kasar ta Sri-Lanka ta ce za a iya samun sakamakon zaben a gobe Lahadi, zaben da mutane miliyan 17 suka cancanci kada kuri'a.