1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Deby ya lashe babban zaben Chadi

April 20, 2021

Alkaluman sakamakon zaben shugaban kasa da aka gudanar a Chadi, na nuni da cewa shugaba Idriss Deby Itno ya sake lashe zaben da gaggarumin rijaye.

https://p.dw.com/p/3sFyg
Tschad N'Djamena | Präsident Idriss Deby Itno im Wahlkampf
Hoto: Renaud Masbeye Boybeye/AFP/Getty Images

Nasarar da Deby ya samu za ta ba shi damar cigaba da mulkin kasar karo na shida. An dai sanar da sakamakon zaben a hukumance, inda Shugaba Deby ya samu galaba da kaso 79 cikin dari na kuri'un da aka kada a ranar 11 ga watan Apirilun da muke ciki. Wannan sanarwar na zuwa ne bayan wani atisayen da dakarun sojin kasar suka yi a manyan titunan babban birnin kasar na N'Djamena.

Sai dai madugun yan tawayen kasar Mahamat Mahadi Ali ya zargi Faransa da daure wa shugaba Daby gindi da ma zama kanwa uwar gami a Chadin.