1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An bude taron tattalin arziki a birnin Davos

Gazali Abdou Tasawa LMJ
January 21, 2020

An bude babban taron tattalin arzikin duniya karo na 50 a birnin Davos na kasar Switzerland, wanda ya samu halartar shugabannin kasashe da na kamfanoni da sauran masu ruwa da tsaki.

https://p.dw.com/p/3WYdX
Schweiz Weltwirtschaftsforum 2020 in Davos
Shugaba Donald Trump na Amirka a taron DavosHoto: Reuters/D. Balibouse

A jawabin da ta gabatar a zauren taron shahararriyar matashiyar nan mai fafutukar kare muhalli Greta Thunberg ta bayyana rashin gamsuwarta da yadda ta ce har yanzu babu wani abin a zo a gani da kasashen duniya suka yi wajen kare muhalli duk da taruka da ake ta gudanarwa kan batun matsalar sauyin yanayin da ma makudan kudin da kasashe da kamfanoni ke ikirarin kashewa. Sai dai daga nashi bangare Shugaba Donald Trump na Amirka ya yi gugar zana ga 'yan fafutukar kare muhallin, wadanda ya kira da 'yan mugun fata ga makomar muhallin duniya da yada labaran karya kan tashin duniya. Trump ya kuma bayyana cewa yana alfahari da yadda tattalin arzikin Amirka ke kara bunkasa fiye da yadda duniya ke tsammani. A bara dai Trump bai jima a wajen taron ba ya kama gabansa, sai dai a wannan karon ana tsammanin zai gana da shugabannin wasu kasashe da suka hadar da Iraki da Pakistan a gefen taron.