David Cameron ya yi murabus daga majalisa
September 12, 2016Talla
Tsohon Firaiministan Birtaniya David Cameron ya yanke hukuncin sauka daga mukaminsa na majalisar dokoki a wata sanarwa da ya fidda a wannan Litinin din inda labarin ya zo wa 'yan Burtaniya din da ba zata. A farko dai David Cameron ya fara yin murabus ne a matsayin sa na Firaiminstan Birtaniya a watan Yuni bayan da ya gaza shawo hankalin 'yan kasar da ga kudirin su na yin zaben raba gardama na ficewa daga tarayyar turai, dama dai Cameron ya kudiri aniyar raba kansa da shugabanci a mulkin jam'iyar Consertive da ake ganin Theresa May ke rowa da tsaki a batun raba gari da kungiyar EU.