1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Isara'ila: Neman taimakon mazauna Gaza

Lateefa Mustapha Ja'afar
October 24, 2023

Sojojin Isra'ila na rarraba wasu takardu a yankin Zirin Gaza na Falasdinu, inda suke bukatar Falasdinawa su ba su bayanan Isra'ilawan da kungiyar Hamas ta yi garkuwa da su.

https://p.dw.com/p/4XyOm
Zirin Gaza | Faladinawa | Sojoji | Isra'ila | Taimako | Ceto | Garkuwa
Sojojin Isra'ila sun zuba takardun neman taimakon Falasdinawan yankin Zirin GazaHoto: Abed Zagout/Anadolu/picture alliance

Sakon dai na kunshe da cewa: "In har kuna fatan zaman lafiya da kuma kyakkyawar rayuwa a nan gaba ga 'ya'yanku, ku yi taimakon jin-kai nan take ta hanyar bayyana mana abin da kuka sani kan Isra'ilawan da aka yi garkuwa da su a unguwanninku. Sojojin Isra'ila sun yi muku alkawarin saka muku da ba ku tsaro da kariya da kuma hasafin kudi har ma da sirranta bayananku. "Kimanin Isra'ilawa 200 ne kungiyar Hamas da ke gwagwarmaya da makamai a yankin Zirin Gazan ta kama kuma take garkuwa da su, yayin harin ba-zatan da ta kai Isra'ila da ya halaka mutane 1,400 a ranar bakwai ga wannan wata na Oktoba da muke ciki.