1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin Darasin Rayuwa

Binta Aliyu Zurmi LMJ
October 9, 2020

Shiri ne da ya yi nazarin halin da al'umma ta tsinci kanta a ciki sakamakon bullar annobar coronavirus da ta mamaye duniya. A wannan mako: Nazari kan yadda kwalli ke hana wasu matan sanya takunkumi a fuskarsu, domin kariya daga annobar coronavirus.

https://p.dw.com/p/3jd2x

A wannan lokacin da saka makarin rufe baki da hanci domin kariya ga annobar coronavirus ya nemi wuri ya zauna a cikin rayuwar alumma, kwalliyar fuska na hana mata saka wannan takunkumin. A wani abun da suka ce yana hana su nuna kwalliyarsu dama lalata ita kwalliyar, to wannan shi ne batun da shirin Darasin Rayuwa na wannan makon zai duba, wane kalubale mata da 'yan mata ke fuskanta wajen rufe kwalliyarku da wannan makarin?