1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsaron Najeriya: Yan kasar mazauna Amirka sun koka

December 28, 2021

Yan asalin Najeriya mazauna Amirka sun sake yin kira ga gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da ta sauke nauyin da ke kanta, na tabbatar da tsaron rayukan al’umma.

https://p.dw.com/p/44vhs
Nigeria Protest gegen der Unsicherheit
Hoto: Nasiru Salisu Zango

Cikin wata sanarwa da Kungiyar DANGI USA ta fitar a birnin Washington, kungiyar ta yi Allah wadai da sakacin da gwamnatin Najeriya take yi, a yayin da ake ci gaba da kashe rayukan talakawa, da barnata da dukiya da satar mutane ba kaukautawa, musanman a yankin arewacin kasar. 

DANGI ta ce, batun yin shawarwari da ‘yan ta’adda ya kare, ya zama wajibi gwamnatin Buhari ta daura damarar yaki gadan-gadan, ta darfafi wadannan bata-gari a ko ina suke, sannan kuma tsoron me gwamnatin take yi, da za ta ki fallasa masu tallafawa ‘yan ta’addar duk karfinsu da tasirinsu?

DANGI USA ta ce, idan kuma gwamnati ta gaza, to gara ta fito fili ta fadawa talakawa, sannan majalisun jihohi da na tarayya su kafa dokokin da za su bai wa ‘yan Najeriya izinin kare kansu da kansu.

Hajiya Hafsat Maina na daya daga cikin ‘yan gwagwarmaya da suke jagorantar zanga-zangar da aka gudanar a Amirka, ta kuma baiyana bacin rai akan gallazawar da ake yi wa talakawa a Najeriya.

Kungiyar DANGI ta ce, kodayake akwai jami’an tsaro masu kishi da suke son yin aikin ceto Najeriya, amma ya zama wajibi, su ma sauran ‘yan kasa, su rika taimaka masu, sannan a rika hukunta dukkan ‘yan ta’addar da aka kama ba wai a saki wasun su ba.

Daga karshe kungiyar ta ‘yan arewa mazauna Amirka, ta sake yin jaje da nuna alhini ga dukkan mazauna Najeriya musanman a arewacin kasar da suke shan ukuba da kuma wadanda suka rasa 'yan uwa da danginsu.