1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dangantakar Masar da ƙasashen Turai

Tijani LawalJanuary 25, 2012

A cikin sharhin da ya rubuta Mudhoon Loay yayi nuni da cewar taimakon da Jamus da sauran ƙawayenta na Turai suka ba wa juyin-jiya-halin ƙasashen Larabawa ba zai yi tasiri ba sai tare da canjin dangantakarsu

https://p.dw.com/p/13pqF
Demonstrators take part in a protest marking the first anniversary of Egypt's uprising at Tahrir square in Cairo January 25, 2012. REUTERS/Mohamed Abd El-Ghany (EGYPT - Tags: POLITICS CIVIL UNREST)
aaaaaaMurnar zagayowar shekara ɗaya da kifar da mulkin Hosni Mubarak a ƙasar masarHoto: Reuters

Juyin juya halin da aka gabatar a ƙasashen Larabawa misalin shekara ɗaya da ta wuce ya zo wa Jamus da sauran ƙasashen Turai a ba zata. Sai dai kuma bisa saɓanin yadda wasu ke zato, wannan boren ba ta sanya Jamus tayi watsi da matakanta na taimako ba. Gwamnati ta taimaka wa juyin-juya-halin neman demokraɗiyyar, musamman ma ƙungiyoyin da suka taka muhimmiyar rawa akan manufa, kuma ɗariɗarin da Jamus ta nunar dangane da yaƙin Libiya bai yi wani tasiri akan matsayin ƙasar ba.

Early days of the Egyptian revolution , army protect the pepole in El-Tahreir Sq. 08.02.2011 - copyrights Amr S. El-Kady
Bukukuwan juyin juya hali a MasarHoto: Amr S. El-Kady

Taimakon gaggawa da Jamus da sauran ƙasashen Ƙungiyar Tarayyar Turai suka ƙaddamar ya kasance wata muhimmiyar madogara ga masu juyin-juya-halin, musamman ma ta la'akari da munana hanyoyin sadarwar dake akwai a waɗannan ƙasashe. Kazalika tayin taimakon da suka yi na kafa sabbin jam'iyyun siyasa da ƙungiyoyin ƙodago da ilimantarwar siyasa, saboda sune ainihin shikashikan mulkin demokraɗiyya tsantsa. Amma fa ba za a fahimci shi kansa muhimmancin juyin-juya-halin ga ƙasashen Turai da ma Jamus ba sai an ba da wata sabuwar fassara ga dangantakar ƙasashen ƙungiyar ta Tarayyar Turaida ƙasashen Larabawa. Akwai buƙatar shiga tattaunawa mai zurfi a game da irin alƙiblar da za a fuskanta nan gaba a dangantaka tsakanin sassan biyu, musamman ma ta la'akari da cewar mutane da dama a nan Jamus da sauran ƙasashen Turai suna ɗariɗari tare da fargabar ci gaban da ake samu a ƙasashen Larabawa. A sakamakon haka kiran da ministan harkokin wajen Jamus Guido westerwelle yayi baya-bayan nan a game da naƙaltar wannan ci gaba da idanun basira ya zama mai muhimmanci bisa manufa. Dangane da ci gaban da jami'iyyu masu kishin addinin musulunci suka samu a ƙasashen Tunesiya da Maroko da Masar, ministan cewa yayi, mayar da manufofin ƙasa kan turbar musulunci baya fa nufin koma baya da ƙyamar demokraɗiyya da rashin walwala. Wannan bayanin nasa ka iya zama tubalin canza salon tunanin ƙasashen Turai.

El-Tahreir Sq. 8-2-2011 Early in the revolution day, a poor man looking to the future. - copyrights Amr S. El-Kady
Akwai buƙatar taimako domin ɗorewar demokraɗiyya a ƙasashen LarabawaHoto: Amr S. El-Kady

Muddin ana fatan kwalliya ta mayar da kuɗin sabulu dangane da taimakon da Jamus da sauran ƙasashen Turai to kuwa wajibi ne ƙasashen na Turai su ba da gudummawa ta gaggawa domin kyautata makomar jin daɗin rayuwar al'umar ƙasashen da lamarin ya shafa ta yadda mulkin demokraɗiyyar zai ɗore kuma murna ba zatab sake komawa ciki ba. Wajibi ne ƙasashen Turai su karɓi ƙasashen Larabawan dake cajin manufofinsu da hannu biyu-biyu su kuma dawo daga rakiyar manufofinsu na mayar da hankali kacokam akan ƙasashen gaɓar tekun bahar-rum da sauran ƙasashe maƙobta. Wannan sabuwar manufar ta jiɓanci canje-canje a ɓangarori na tattalin arziƙi da zamantakewa daidai da halin rayuwa da al'umar ƙasashen ke ciki. Hakan kuwa ta haɗa da buɗe ƙofofin kasuwannin ƙasashen Turai ga amfanin noman da ƙasashen ke samarwa da karɓar ƙwararrun ma'aikata 'yan ci-rani. Irin wannan matakin zai iya taimakawa wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a waɗannan ƙasashe.

Mawallafi: Mudhoon Loay/Ahmad Tijani Lawal

Edita: Usman Shehu Usman