1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matakin kare bayanan EU da Japan

Lateefa Mustapha Ja'afar
September 5, 2018

Kungiyar Tarayyar Turai da kasar Japan na shirin daukar matakin kulla yarjejeniyar tabbatar da kare bayanai, da nufin karfafa dangantakar kasuwanci da ke tsakaninsu.

https://p.dw.com/p/34Luy
Japan Tokyo - Donald Tusk, Shinzo Abe und  Jean-Claude Juncker
Shugaban kungiyar EU Donald Tusk da Firaministan Japan Shinzo Abe da kuma shugaban hukumar kungiyar ta EU Jean-Claude JunckerHoto: picture-alliance/AP Imags/T. Joko

Hukumar Tarayyar Turan ce ta sanar da hakan, inda ma ta fitar da wani jadawali da ke dauke da jerin ka'idojin da za a yi amfani da su a duk wani bayani daga Tarayyar Turan da aka tura kasar ta Japan, ciki kuwa har da bayanai da suka shafi jami'an tsaro da kuma hukumomin tsaron Japan din, matakin da hukumar ta ce hakan zai kare duk wani bayanai na 'yan kasashen na EU a Japan tamkar yadda ake kare bayanansu a Tarayyar Turan.