1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Makomar dangantakar Saudiyya da Amirka

Knipp Kersten/ Umaru Aliyu/ YBApril 20, 2016

Ziyarar da Shugaba Barack Obama ya kai kasar ta Saudiyya ba za ta zama mai sauki ba, musamman bisa lura da sabanin da ke tsakanin kasashen biyu a baya-bayan nan.

https://p.dw.com/p/1IZ8v
Saudi-Arabien König Salman empängt Barack Obama
Shugaba Obama da Sarki Salman na SaudiyyaHoto: Reuters/K. Lamarque

Shugaban Amirka, Barack Obama ya fara ziyarar aiki a kasar Saudiyya daya daga cikin kasashen da a bisa manufa, suka fi kawance da gwmnatin Amirka a Gabas ta Tsakiya. Ziyarar ta Obama, ta zo ne a daidai wani lokaci mai matukar wahala a dangantakar kasashen biyu, inda masana suka ce fahimtar juna da aka dade ana samu tsakaninsu yanzu dai babu sauranta, inda a maimakon haka, wani hali na rashin yarda da juna ya shiga tsakaninsu.

Wannan hali na rashin yarda da juna ya samo asalinsa ne tun daga hare-haren tarzoma na ranar 11 ga watan Satumba 2001 a New York da Washington, inda 15 daga cikin yan ta'adda 19 da suka kai wadannan hare-hare suka kasance 'yan asalin Saudiyya. Tun bayan wannan lokaci mahukunta a Washington suka shiga nuna kyamarsu ga akidar Wahabiyawa da ta yi karfi a kasar. A 'yan makonnin baya a Wasghington, aka sami karin bayani cikin rahoton da aka tsara tattare da hare-haren na 11 ga watan Satumba, inda daya daga cikin 'yan kwamitin bincike da suka tsara wannan rahoto, Bob Kerry ya ce babu shakka ba za mu tsame Saudiyya gaba daya daga cikin masu laifi ba.

A daya hannun, Saudiyya na iyakacin kokarinta domin samun damar karanta abin da ke kunshe a wannan rahoto. Tsohon ministan harkokin wajen kasar Saudiyya al-Faisal tun a shekara ta 2003 ya ce idan har cikin rahoton ana zargin Saudiyya da wani laifi, to kuwa ya kamata a ba ta damar ganin abin da ke cikinsa, yadda za ta mayar da martanin da ya dace. Har ya zuwa yau, kasar ba ta sami damar karanta wannan rahoto ba.

Saudi-Arabien König Salman empängt Barack Obama
Shugaba Obama da mai masaukin bakinsaHoto: Reuters/K. Lamarque

A irin wannan hali, ziyarar da Barack Obama ya kai kasar ta Saudiyya ba za ta zama mai sauki ba, musamman bisa lura da sabanin da ke tsakanin kasashen biyu a baya-bayan nan. Sebastian Sons, masani kan yankin Gabas ta Tsakiya na cibiyar nazarin al'amuran ketare ta Jamus, ya ce Saudiyya na ganin Amirka ta yi watsi da ita a daidai lokacin da take bukatar taimako da goyon baya.

" Musamman hakan ya fi fitowa fili sakamakon yarjejeniyar atom da aka cimma da Iran, wadda ita ce babbar abokiyar adawar Kasar Makka a wannan yanki. Bugu da kari kuma, Amirka din tana ci gaba da nuna dari-dari game da taimaka wa kamfe da sojojin Saudiyya suke yi a kasar Yemen. Haka nan kuma, bukatu da manufofin kasashen biyu game da Siriya ko kadan ba su dace da juna ba. Yayin da Saudiyya take neman kawar da mulkin Bashar al-Assad, Amirka tana janye jikinta daga wannan bukata".